Wannan manhajar na ɗauke da ingantattun zikirori da addu'o'i daga Alƙur'ani da sunna, waɗanda aka ciro su daga cikin ingantattun littattafai.
Sannan tana ɗauke da mas'aloli da suka shafi zikiri waɗanda malamai suka yi bayani akai. Da wasu abubuwan na daban da suke da alaƙa da zikiri.
*Abubuwan da suke ciki
1) Zikirin safiya da maraice
2) Zikirin da ake yi a cikin salla
3) Zikirin bayan an yi sallama daga salla
4) Falaloli
5) Littafin Hisnul Muslim
6) Mas'aloli game da zikiri:
- ladubban yin addu'a
- Lokuta da halaye da kuma yanayin da aka fi amsa addu'a a cikin su
- Amfanin ambaton Allah
- Wuraren da Allah Maɗaukaki yafi amsa addu'a
- Mafiya muhimmancin addu'o'in da mutum ya kamata ya roƙa a wajen Allah Maɗaukaki
Da sauran su.
* Muhimman abubuwan da manhajar ta keɓanta da su (features)
1) Arabic tare da fassara
2) Audio domin sauraron addu'a, ba tare da an kunna data ba
3) Nemo addu'a cikin sauƙi, ta hanyar rubuta wani sashi na sunan addu'ar
4) Kalar screen mara haske domin kariyar ido
5) Tura addu'a kai tsaye zuwa wata manhajar
Da sauran su.
* In sha Allah zamu ci gaba da bunƙasa wannan manhajar lokaci bayan lokaci.
* Domin yin tarayya a cikin wannan aikin don samun lada, ka tura wannan manhajar zuwa ga sauran ƴan uwa Musulmai
* Za a iya tuntuɓar mu ta Gmail ga mai buƙatar wani abu:
[email protected]